Da soma zaman kwamitin binciken gwamnan jihar Adamawa da mataimakinsa, sai gashi 'yan majalisar jihar na zargin cewa ana yiwa rayuwarsu barazana.
Sakataren yada labaran majalisar Mr. Solomon Kumanga yace sun bankado wani yunkurin kai masu hari tare kuma da sace wasunsu. Amma yace yunkurin ba zai razanasu ba. Yace wai an kawo 'yan bindiga dadi su harbesu su ko kuma su sace wasu domin kada su iya cigaba da gudanar da binciken da aka soma yanzu. Kakakin yace sun samu hujjoji daga jami'an tsaro da wasu mutane.
A cewar kakakin wai ana rabar da hotunan 'yan majalisar domin su 'yan bindigar su ganesu su kuma hallakasu ba tare da yin kuskure ba tunda basu san 'yan majalisar ba. An dauki matakan tsaro. Kowane dan majalisa an tura masa jami'an tsaro domin kare lafiyarsu.
To saidai jam'iyyar APC ta bakin kakakinta Mr. Sabio ta mayar da martani inda tayi watsi da zargin 'yan majalisar. Kakakin yace duk lokacin da mutum ya taka doka dole ya ji tsoro. Ko inuwarka na iya baka tsoro domin ka san baka aikata daidai ba. Su 'yan majalisar sun sani cewa abun da suke yi ba domin jihar Adamawa su keyi ba. Duk abun da aka yi bisa zalunci dole a tsorata.
Ita ma rundunar 'yansandan jihar ta bakin kakakinta DSP Usman Abubakar tace bata da masaniya akan yunkurin amma ta dauki duk matakan kare rayuka da kuma dukiyoyin jama'a.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5