A firar da yayi da wakilin Muryar Amurka Onarebul Ibrahim Bello ya bayyana dalilan da suka sa suka kafa dokar bada katin zabe na wucin gadi ga wadanda suke gudun hijira ko wata matsala ta rabasu da gidajensu.
Majalisa tana so ta baiwa mutane da suka afka cikin wani bala'i kamar na jihohin Borno, Adamawa da Yobe da yanzu suke sansanonin 'yan gudun hijira su samu damar kada nasu kuri'un. Daga bisani kuma idan sun koma gidajensu sai a basu katin zabe na dindindin. Wajibi ne a bisu inda suke su samu su jefa kuri'a.
Akan wai lokaci ya kure domin kafin shugaban kasa ya sa hannu a dokar lokacin zaben yayi sai dan majalisar yace su dai sun yi nasu aikin sauran kuma ya rage ga shugaban kasa.
Wadanda suke gudun hijira sun gwammace gwamnati ta taimaka masu su koma gidajensu ba zabe ya damesu ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5