Jami’an kashe gobara na samun dan ci gaba wajen kokarin dakile gobarar da ta shafe daukacin unguwanni a birnin Los Angeles na Amurka.
Ya zuwa safiyar Assabar, an sami shawo kan kashi 43% na harsunan wutar Palisades, wanda ya karu daga kashi 31% na ci gaban da aka samu a ranar Juma'a, a cewar Ma'aikatar Gandun daji da Kariyar gobara ta jihar California.
Gobarar ta kone kusan kadada 10,000 na fili.
A halin da ake ciki kuma, an sami cin karfin harshen wuta na Eaton da 73% a safiyar Asabar, daga 65% da aka samu a ranar Juma'a, a cewar hukumar. Wutar Eaton ta kone sama da hekta 5,700 na fili.
Harsunan gobarar guda biyu sun kashe akalla mutane 27 tare da lalata gine-gine sama da 12,300.
Ofishin shugaban ‘yan sandan Los Angeles ya fada a ranar Alhamis cewa, mutane 18 sun bace sakamakon gobarar.
Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya shaidawa gidan talabijin na NBC a wata hira da aka yi da shi a ranar Assabar cewa, mai yiwuwa zai je yankin a karshen mako mai zuwa.
Gwamnan California Gavin Newsom a makon da ya gabata, ya gayyaci Trump ya ziyarci yankin.