'Yan Kwallon Afirka Da Tauraruwarsu Ta Haska A Turai A Wannan Makon

  • Murtala Sanyinna

Sadio Mane

Dan wasan gaba na Liverpool Sadio Mane ya zura kwallon ta 20 a wannan kakar wasanni, a wasan gasar Premier da Liverpool din ta yi nasarar doke Aston Villa da ci 2-0 a filin wasanta na Anfield.

Sadio Mane


Wannan ne shekara ta 3 a jere da dan wasan dan kasar Senegal, wanda yanzu haka shi ne gwarzon dan kwallon Afirka, ya ke zurawa kungiyar kwallaye akalla 20 a kakar wasanni.

Wani dan wasan Afirka da tauraronsa ya haska shi ne dan Najeriya Kelechi Iheanacho na kungiyar Leicester City, wanda shi ma ya zura kwallo a wasan da kungiyar ta doke Crystal Palace da ci 3-0.

Kelechi Iheanacho

A kasar Spain kuma matashi mai shekaru 17 dan kasar Guinea-Bissau Ansu Fati, ya zura kwallonsa ta 7 wa kungiyarsa ta Barcelona, a wasan da ta yi galaba akan Villarel da ci 4-1.

Fati dai ya shiga wasan ne daga baya a matsayin canjin wani dan wasa, ya kuma zura kwallon da ta taimakawa Barcelonar rage tazarar maki tsakanin ta da Real Madrid zuwa 4 a gasar La Liga ta kasar.

Ansu Fati


Haka shi ma dan wasan baya na kungiyar Real Betis Zouhair Feddal dan kasar Morocco, ya ceto kungiyar daga shan kashi ta kuma sami maki daya, a yayin da ya zura kwallon da ta farke wadda Celta Vigo ta yi a wasarsu ta La Liga da ta karkare da kunnen doki da ci 1-1.

Zou Feddal


A kasar Italiya kuma ‘yan kasar Gambiya biyu, Musa Juwara da Musa Barrow, sun taka muhimmiyar rawa a wasan da kungiyarsu ta Bologna ta yi waiwayen baya ta doke Inter Milan da ci 2-1 a wasan gasar Serie A.

Musa Juwara

Musa Barrow


Musa Juwara da ya shiga wasan a zaman canji, ya zura kwallon da ta daidaice da kwallon da Inter din ta zura a minti na 74 na wasana, kafin shi kuma Musa Barrow ya zura ta shi kwallon a mintunan karshe na wasan, wadda ta baiwa kungiyar ta su ta Bologna nasara.