Rundunar sojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole ta ce wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi shigar burtu, a matsayin masu bayar da agajin gaggawa a garin Gudunbali dake arewacin Borno.
Maharan dai sun kai harin ne ranar Juma’a, ta hanyar amfani da yadda ake raba kayan agaji a garin Gudunbali, wanda hakan yasa suka yi shigar burtu.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar Operation Lafiya Dole ya sanya wa hannu, ta ce maharan sun shiga garin ne cikin wata babbar motar daukar kaya, inda nan take jami’an soja suka mayar musu da martani.
Sanarwar ta ce an kashe da yawa daga cikin ‘yan Boko Haram, an kuma gano makamai masu yawa.
A daya bangaren kuma, tun farko rundunar sojan ta fitar da wata sanarwa dake zargin asusun tallafawa kananan yara na MDD, dake aiki a shiyyar arewa maso gabashin kasar.
Rundunar sojan dai ta ce Asusun tallafawa kananan yaran na daga cikin wadanda ke kawo cikas a yakin da ake da kungiyar Boko Haram.
Inda aka zargi asusun da horas da wasu ma’aikata domin leken asiri kan yadda sojojin ke gudanar da aikinsu, don haka rundunar sojan bata yar da aikin da Asusun ke yi a shiyyar ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5