‘Yan Kasuwar da suka yi hasara a sakamakon gobarar kasuwar Sabon Gari Zasu Sami Tallafi

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umaru Ganduje

Kimanin shekaru biyu bayan gobarar da akayi a kasuwar sabon Garin Kano, wadda ta lalata dukiyar ‘yan kasuwa ta kusan Naira biliyan 25,za’a rabawa ‘yan kasuwar da suka yi hasara kudaden tallafi da hukumomi da kungiyoyi suka ba su ta hannun gwamnatin Kano.

Dr Abdullahi Umar Gandujegwamnan Kano ya bayyana jimllar kudin da aka tarada suka hada da Naira miliyan 500 daga Alhaji Aliko Dangote da kuma gwamnatinsa wadda ita ma ta bayar da Naira miliyan 500 yayin wani kwarkwayan taro na karbar cakin kudi mai kunshe da naira miliyan dari biyar gudunmawa daga Alhaji Aliko Dangote. Gwamnan yace kawo yanzu an tara Naira biliyan daya da miliyan dari biyu.

Ko a litinin din nan kafofin labaru na cikin gida sun ruwaito gwamnan na Kano na alakanta gobarar ta kasuwar sabon Gari da matsala irin ta wayar lantarki. Kodayake tun lokacin da lamarin ya faru kamfanin samar da wutar lantarki mai kula da jihohin Kano, Jigawa da Katsina, KEDCO ya nesanta kansa da gobarar.

To amma Alhaji Abdulkadir Bala Madigawa dake zaman wakilin ‘yan kasuwar ta sabon Gari a kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin binciko musabbabin gobarar na cewa sakamakon binciken da suka gudanar ya nuna wutar lantarki ce ta jawo gibarar. Ya yi kira ga gwamnati ta taimaka masu da abun da ya sawaka. Haka ma ya yi kira ga kamfanin KEDCO ya biyasu diyya gameda abun da ya faru.

Dangane da kudaden da aka tara domin tallafawa ‘yan kasuwar gwamna Ganduje ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba kwamitin da gwamnati ta kafa zai zauna ya rabawa ‘yan kasuwa kudin da aka tara.

Galibin ‘yan kasuwar da wannan iftila’i ya shafa dai sun ma fara fitar da rai da samun wancan tallafi.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Wadanda Gobarar Kasuwar Sabon Gari Ta Shafa Zasu Sami Tallafi - 2' 34"