Yan Kasar Kenya Sun Kada Kuri'u Zaben Sabon Shugaba Yau Talata

Shugaba yan adawan kasar Kenya Raila Odinga wanda yake neman shugabancin kasar a karkashin jami'iyyar NASA ya kada tashi kuri'ar a makarantar firamare dake Kibera, Nairobi.


 

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta na gaida mago bayansa bayan kada kuri'arsa a garinsu, Gatundu dake Kiambu.

 

Wani dan gidan kaso ya kada tashi kuri'ar a gidan kurkukun Kamiti dake kusa da babban birnin kasar.


 

Kabilar Masai sun kada nasu kuri'u a garin Bissil dake da tazarar kilometa 120 da babban birnin Nairobi.

 

'Yan kasar Kenya masu kada kuri'u  a wata runfar zabe da kårfe 6 na safe a yankin Westland dake birnin Nairobi.

 

Zaben shugaban kasar Kenya na shekarar 2017.

 

Wasu mata da iyalansu a Gatundu dake garin Kiambu a kasar Kenya.

 

Tsohon sakataran harkokin wajen Amurka John Kerry tare da firaminstan kasar Senegal Amina Toure daga cibiyar masu sa ido a zabe ta gidauniyar  Carter sun yi tattaki zuwa makarantar Westands dake Nairobi.

 

Lydia Gathoni Kiingali mai shekaru 102 ita ma ta jefa kuri'arta a runfar kåda kuri'u dake Gatunda a arewacin Birnin Nairobi.


 

Runfunan Zaben shugaban kasar Kenya na shekarar 2017 a tsakiyar birnin Nairobi.

 

Mutane sun yi layi a filin ajiye motocin domin su kada tasa kuri'u a tsakiyar birnin Nairobi.