Taron ya gudana ne a wani lokacin da kasashen duniya ke bukukuwan tunawa ranar Hausa ta duniya a yau Litinin 26 ga watan Agusta karo na 9.
La’akari da matsayin harshen Hausa a fannin sadarwar jama’a a nahiyar Afrika da kuma tasirin harshen a harakokin watsa labarai ya sa kungiyar hadin kan ‘yan jarida masu aiki da Hausa ta shirya wannan taro da ya sami halartar tawwagogin kasashe 11 inda aka tattauna akan batun zaman lafiya. Mariama Laouali Sarkin Abzine ita ce shugabar wannan kungiya.
A tsawon kwanaki biyu na wannan zama an gabatar da laccoci kan illolin da amfani da kafafen sadarwa na zamani ta gurabtacciyar hanya ke yi wa sha’anin zaman lafiya a wannan lokaci da masu mummunar farfaganda suka mamaye sha’anin sadarwa da zummar cimma tasu manufar. Isa Abubakar Shuni Sokoto na daga cikin mambobin tawwagar Najeriya.
Wata kididdiga kan harsunan da aka fi amfani da su ya yi nuni da cewa Hausa ce harshe na 11 a duniya. Abdoulkarim Anisce wani dan jarida dake aiki a yankin Agadez na ganin wannan haduwa a matasyin ta kara jan damarar ayyukan waye kan al’umma ta hanyar kafafen labarai.
Daga cikin shawarwarin da aka tsayar kungiyar ta kudiri aniyar samar wa ‘yan jaridar Hausa damar gudanar da aiki cikin kyakkyawan yanayi.
Da yake jawabin bude taro amadadin shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijer Janar Tiani, Fira minista Ali Lamine Zeine ya yaba da wannan yunkuri . A cewarsa mahukunta sun yi amannar amfani da harshen Hausa hanya ce da za ta taimaka wajen fadakar da jama’a kan mahimmancin zaman lafiya.
Hausa da ke matsayin hanyar sadarwar mutane kusan million 100 na daga cikin harsunan da ke taka rawa a harakokin ci gaban tattalin arziki, yada al’adu, ci gaban ilimi da karfafa cudanya a tsakanin jama’a.
Baicin Najeriya, Nijer, Cameroun, Ghana, Sudan da Chad bincike ya gano cewa Hausa na kara samun gindin zama a manyan biranen kasashen Afrika irinsu Dakar, Cotonou, Abidjan, Bangui, Brazaville, Conakry da sauransu.
Wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma na dauke da Karin bayani cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5