'Yan-Jarida Na Iya Kawo Karshen Cin Hanci Da Rashawa A Duniya

Jabir Mustapha Sambo

Jabir Mustapha Sambo, dalibi dake karatun bunkasa aikin jarida da yadda za'a inganta rayuwar jama'a, a jami'ar 'Robert Gordon Aberdeen' yana ganin cewar idan matasa zasu maida hankali wajen ganin sun samu ilimi, musanman wanda zasu taimaka ma al'ummar yankin su, to babu shakka rayuwar su zata inganta.

Kuma ta haka ne kawai kasa zata iya cigaba, domin kuwa yaga haka a iya zaman shi da yake a kasar Birtaniya, wanda matasa a baki daya kasar basa zaman banza, suna aiki tukuru wajen biyan bukatun kansu da kuma nemo hanyoyi da za suyi wani abu da al'umar su zasu amfana da ilimin su ko kuruciyarsu.

Jabir Mustapha Sambo

Hakan ma yakan sa matasa yin abubuwa da tarihi bazai manta da suba a kasar, wajen kirkirar wasu abubuwa da jama'a zasu amfana dashi don ace mutun yayi shi, kamar misali idan aka duba abun da mai kamfanin Facebook Mark Zuckerberg, yayi wanda baki daya duniya ke cingajiyar basirar shi.

Wannan shine abu da ya kamata ace matasan Najeriya koma ace Afrika baki daya sun maida hankali akai. Sai a saurari karashin tattaunawar a kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan-Jarida Na Iya Kawo Karshen Cin Hanci Da Rashawa A Duniya 2'20"