Yanzu dai tunanen mutane ya sauya akan Nuhu Ribadu wanda ya canza sheka daga APC zuwa PDP. Mutane na ganin shigarsa PDP zata sa ya samu tsayawa takarar ba hamayya. Yanzu ba haka batun yake ba.
Kawo yanzu 'yan takara fiye da goma ne daga PDP suka fito suna neman kujerar gwamnan. Wadanda suka fito sun hada da mukaddashin gwamnan Umaru Ahmed Fintiri da tsohon minista Idi Hong da tsohon mai ba shugaba Jonathan shawara akan siyasa Ahmed Gulak.
Idi Hong wanda ya koma gefe tun lokacin da ya rasa kujerar minista shekaru hudu da suka wuce yace ya shirya tsaf domin tsayawa. Kamar yadda ya bayyana babu lungun kananan hukumomi ashirin da biyu na jihar da bai shiga ba. Jihar na neman jarumi wanda yake da basira da kuzari da kuma karfin yi mata shugabanci. Yace kuma duk wadannan abubuwa da yaddar Allah yana dasu.
A nashi bangaren Barrister Ahmed Gulak yace matukar ya samu tikitin PDP din to tamkar an gama. Yace yana gayawa mutane kullum cewa APC ba jam'iyya ba ce. Jam'iyya ce ta karo-karo wadda bata san ka'idarta ba. Wai jam'iyyar APC din ma ta fashe. Misali a arewa ina Bafarawa, ina Shekarau, ina Buba Marwa, ina Gundiri kuma an ce Nuhu Ribadu ya shiga PDP. Dukansu sun watse sun koma PDP. Mutanen dake Abuja basu san abubuwan dake faruwa a jihar ba.
Za'a yi zaben maye gurbin gwamnan a ranar sha daya ga watan Oktoba inda yanzu PDP na sayar da takardar neman takarar akan nera miliyan goma sha daya. APC kuma na sayar da nata akan nera miliyan biyar da dubu dari biyar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5