'Yan Hamayya A Senigal Sunyi Kira A Fara Zanga Zanga Ta Gama Gari

Gungun matasa dake zanga zangar nuna kyamar shirin sake takarar shugaba Wade.

Kungiyoyin hamayya a Senigal dake yammacin Afirka, sun yi kira da a yi zanga-zangar gama gari a duk fadin kasar yau talata, domin......

Kungiyoyin hamayya a Senigal dake yammacin Afirka, sun yi kira da a yi zanga-zangar gama gari a duk fadin kasar yau talata, domin bayyana rashin goyon baya kan yunkurin tazarce, da shugaba Abdullahi Wade na kasar yake shirin yi, a zaben kasar da za a yi cikin watan gobe.

Shugaban dan shekaru 85 da haifuwa, yana mulkin kasar tun 2000. Shekara daya bayan yah au mulki, aka yi wa tsarin mulkin kasar kwaskwarima, wadda ya taikata wa’adi biyu ga shugabancin kasar. Duk d a haka Mr. Wade ya dage cewa, wan nan canji bai shafeshi ba, ganin an kaddamar da canjin ne bayan ya fara mulki.

Kotun tsarin mulkin kasar ta goyi bayansa kan haka.

Wan nan shawara ta janyo zanga zanga da aka fara cikin makon jiya, wadda yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a garin Podor, dake arewacin kasar. Shaidun gani da ido suka ce jami’an tsaro ne suka ce wata mace, da kuma wani dalibin makarantar sakandare,a jiya litinin.

Idan za’a iya tunawa, ranar juma’a data shige aka kashe wani jami’in dan sanda a wani mummunar zanga zanga d a aka yi a Dakar, babban birnin kasar.

‘Yan kasar Senigal akan titunan birnin Dakar da suka zanta da wakilin Muriyar Amurka, baki daya sunyi itifakin cewa shugaba Wade yayi murabus. Galibin ‘yan kasar sunce ya tsufa yaci gaba da mulki. ‘Yan hamayya suka ce zasu ci gaba da fafatawa da shugaba Wade, har ranar zabe, 26 ga watan Febwairu.

Sakamakon tarzomar a Senigal, Amurka da Faransa sun bayyana damuwa. Mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka William Burns, ya gayawa manema labarai a Addis Ababa cewa, shawarar da Mr. Wade ya yanke na sake yin takara yana barzana ga tarihin da Senigal take dashi na zaman lumana na lokaci mai tsawo.