'Yan gudun Hijira Na Ci Gaba Da Shiga Turai

A lokacin da ake ceton wasu 'yan gudun hijra daga gabar tekun Italiya a yankin Lempadusa

Rahotanni sun ce 'yan gudun hijrar na samun saukin ratsawa ta kasar Hungary fiye da yadda abin ya kasance a makon jiya, lokacin da aka ga alamar dai wannan kasa ta yankin tsakiyar Turai na shirin yin komai don hana 'yan gudun hijirar shiga kasashen Yammacin Turai mafiya arziki.

A yanzu 'yan Hungary na ma tallata tafiyar jiragen kasa zuwa Austria ga 'yan gudun hijirar da ke tashar Keleti ta Budapest. A makon jiya har jefa barkwanon tsohuwa 'yan sanda ke yi kan 'yan gudun hijirar da ke tashar ta Keleti masu niyyar zuwa Austria.

Wani ganau ya ce "yanzun nan ma" aka cika wasu jirage masu zuwa Austria da 'yan gudun hijirar.

Da sun isa tashar jirgin kasa ta Westbahnhof da ke Vienna, sai 'yan Austria su tarbe su da tafi da jinjina, su ta masu jagora daga wannan jirgin zuwa wancan, a kokarinsu na zarcewa zuwa kasar Jamus. Kadan daga cikin 'yan gudun hijirar ne kan so zama Austria.

Dama da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar na da 'yan'uwa a kasar ta Jamus, wacce ke kiransu da su je su hadu da 'yan'uwan nasu.

Kasar Jamus, wacce ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Turai - ta fadi yau Litini cewa za ta ware karin dala biliyan 6.6 ga bangaren kasafin kudin tallafa ma jama'a don ta tsugunar da 'yan gudun hijirar sosai cikin al'umma. Jamus dai ta ce a shirye ta ke ta dau 'yan gudun hijra 800,000.

Sabbin isan 'yan gudun hijirar kan buga ma 'yan'uwansu da abokansu da ke kan hanyar zuwa waya, ko kuma su masu bayani ta kafar sada zumunci ta FaceBook, game da irin abubuwan da za su tarar a kan hanyarsu ta zuwa Turan.