Yakin da aka kwashe wata guda ana yi a yankin Tigray da ke arewacin kasar Habasha ya kawo cikas sosai a kokarin yaki da cutar coronavirus, daya daga cikin munanan annobar da Afrika ta taba gani, yayin da yakin ya sa mutane kusan miliyan 1 yin gudun hijira lamarin ya kuma kawo cikas sosai a ayyukan jinkai.
Dubban mutane da ke guje wa fadan da ake yi tsakanin dakarun Tigray da Habasha ne suka tsallaka zuwa makwabciyar kasar Sudan, inda nan ma ake samun karuwar yaduwar cutar coronavirus sosai a fadin kasar.
Sama da ‘yan gudun hijira 45,000 da suka tsere wa rikicin Tigray yanzu suke tsugunne a wasu sassan Sudan, inda suke zama a wasu sansanonin da ba a gwajin cutar coronavirus kuma babu cibiyoyin jinyar cutar.
“Yayin da ake fuskantar COVID-19, yanayin shiga wasu motocin bas bai da dadi, a cewar wani dan gudun hijira mai suna Hailem, wanda ya ce sama da mutane 60 suka shiga wata mota da ta kwashe su daga Hamdayet, da ke yankin iyakar Sudan, zuwa sansanonin.”