Babban zabe Najeriya da za a yi a watan biyu na shekara mai zuwa na karatowa. Inda masu kada kuri’a da dama ke korafin har yanzu basu karbi katin din-din-din na zaben ba. Ga wadanda ke cikin salama kenan, ina ga wadanda rikice-rikice suka rabasu da mahallansu, suke gudun hijira zuwa sassa da banda ban na arewacin Najeriya har ma da makwabtan kasashe?
Wasu kuma daga cikin ‘yan gudun hijirar na ganin ba za su sami damar kada kuri’ar ba koma da sunyi rijistar.
Wakilin muryar Amurka yayi hira da wasu, dake gudun hijira yanzu haka a kasar Kamaru, sun fada masa cewa su bukatarsu ita ce a kwato masu garinsu in ana so suyi zabe don kuwa in ba kwanciyar hankali zabe ba zai yiwu ba.
Mataimakin Darektan hulda da jama’a na hukumar zabe Nick Dazan, ya fadi cewa bisa ga tsarin hukumar zabe, kwanaki talatin kafin zabubbukan shekara mai zuwa, masu kada kuri’a na iya zuwa Ofishin su na karamar hukuma don neman takardar kaura daga inda suka yi rijistar zuwa inda zasu iya kada kuri'a.
Your browser doesn’t support HTML5