A Najeriya ‘yan gudun hijira fiye da dubu 50,000 daga jihohin Arewa maso gabas dake zaune a jihar Bauchi, suna fuskantar matsananciyar matsalar rashin abinci. Hukumar bunkasa shiyyar arewa maso gabas ta NEDC ita ce ke da alhakin raba abinci ga ‘yan gudun hijiran a bayan kowanne wata uku.
Bincike ya nuna cewar ‘yan gudun hijiran sun shafe wa’adin da akayi musu alkawari na za a rinka basu abinci a kowanne wata uku, amma ba'a ba su ba, duk kuwa da cewa an kawo kayan abincin har sun soma lalacewa.
Shugaban ‘yan gudun hijiran a jihar Bauchi, Buba Musa Shehu ya shaida wa wakilin muryar Amurka cewa, ‘yan gudun Hijirar suna cikin halin galabaita, ba sa samun abinci kuma an killace su an hana su fita su nemo abincin. Ya ce, kungiyar “North East Development, NEDC” ita ta ke kawo musu abinci, amma a yanzu ba sa samu.
Jami’in raba kayan abincin na hukumar bunkasa shiyyar Arewa maso gabas wato NEDC yayi wa wakilin muryar Amurka Karin bayani ta wayar tarho, inda ya ce har yanzu bai samu umarnin cewa ya rabawa ‘yan gudun hijirar kayan abincin ba, amma ya samu umarnin cewa ya rabawa gwamnatin jiha da ‘yan majalisar tarayya da na dattawa.
A wata sabuwa kuma al’umomin yankunan kananan hukumomin Katagum da Giade da kuma Zaki wadanda aka sanya musu dokar hana fita na tsawon kwanaki goma in banda ranakun Asabar, suna kokawa akan basa samun tallafi abinci.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5