A ranar Litinin 11 ga watan Mayu nan ne hukumar ta EFCC ta damke mutanen guda biyu ‘yan asalin kasar China akan yinkurin bada toshiyar baki ga shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya shiyar Sokoto.
Wadannan mutanen dai wakilai ne na wani kamfani na kasar China da gwamnatin jihar Zamfara ta ba kwangilolin samar da hanyoyi a wasu kananan hukumomi da samar da rijiyoyin burtsatse guda 168 a kanann hukumomi 14 na jihar Zamfara daga shekarar 2012 zuwa 2019 akan zunzurutun kudi sama da naira biliyan hamsin.
Binciken da hukumar ta kaddamar akan kwangilolin shi ne ya zaburar da kamfanin akan ya bada toshiyar baki ta naira miliyan 100 ga shugaban hukumar, inda wakilan kamfanin suka fito da naira miliyan 50 a matsayin rabin kudin da zasu bada na toshiyar bakin.
Abdullahi Lawal shine shugaban hukumar EFCC a shiyar Sokoto, ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike kafin su gurfanar da mutanen a gaban kotu.
Dakta Rufa’i Shehu, masani a harkar tattalin arziki a jami’ar Usman Danfodiyo, ya ce kamen da aka yi wani abu ne mai alfanu a Najeriya duba da irin gwagwarmayar da kasar ke yi wajen samar da ayyuka don morar al’umma. A cewarsa idan har wasu zasu dinga yin zagon kasa suna yin sama da fadi da kudaden kasar to tabbas tattalin arzikin Najeriya zai ci gaba da fuskantar kalubale.
Saurari Karin bayanicikin sauti daga Muhammad Nasir.
Facebook Forum