Cikin kwanaki uku hukumar tayi rajistan mutane fiye da dubu daya daga karamar hukumar Damboa dake cikin jihar Borno.
Shugaban hukumar Dr Danlami Arab Shukudi ya bayyanawa wakiliyar Muryar Amurka cewa cikin kwana uku da suka gabata hukumarsa ta samu fiye da mutane dubu daya kuma har yanzu suna kara isowa garin Gomben. Yadda mutanen ke kwararowa ya fi karfin duk tunanensu a hukumance.
Can tashar Dadinkowa inda motoci ke saukar da mutanen an ga wasu da yawa kara zube. Dr Shukudi tace sai sun tantance mutanen kafin su yi masu rajista. Bayan sun tantance idan an samu gida sai a basu ko kuma kayan tallafi kamar kayan kwanciya da makamantansu da kayan abinci.
Domin a tabbatar cewa bata gari basu shiga lamarin ba akan kai kayan agajin ne wurin masu anguwanni su raba domin su suka san mutanen anguwansu da wadanda suke gudun hijira.
Mutanen Damboan da suka gudu sun ce fada ne ya korosu domin babu wurin da zasu sa kai. Sun sha wahala akan hanya kafin su iso Gombe.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.
Your browser doesn’t support HTML5