'Yan Gudun Hijira da Suka Koma Garuruwansu a Jihar Adamawa Na Shirin Yin Noma

Jihar Adamawa

A karon farko cikin shekaru shida da suka gabata wasu 'yan gudun hijira a jihar Adamawa da suka koma yankunansu suna shirin noma gonakan da suka bari saboda rikicin Boko Haram

Wani daga cikin 'yan gudun hijiran da suka koma garuruwansu yace suna kokari su ga cewa a daminar bana sun samu sun yi noma tunda zaman lafiya ya dawo.

To sai dai suna kiran gwamnatoci kama daga na kananan hukumomi zuwa jiha da na tarayya su taimaka masu da samar masu iri masu nuna da wuri da kuma taki.

A garin Michika inda yawancin 'yan gudun hijiran suka koma sun soma share gonakansu saboda basu da wani damuwa.

Dangane da ko an dasa bama bamai a gonakan nasu sun ce suna sane da yiwuwar hakan saboda ko makon jiya wani yaro ya ci karo da bam a gona amma sun ja kunnuwan mutane idan suna zuwa gona su yi noma to su bi a hankali.

Ita ma gwamnatin jiha tace ta shirya tsaf domin ta sharewa manoman hawaye tare da basu kwarin gwuiwar zama a gidajensu.

Kwamishanan harkokin noma na jihar, Waziri Haruna Ahmadu ya bayyana matakan da gwamnati ke dauka akan wadanda suka koma matsuguninsu. Yace gwamnati zata yi iyakar kokarinta ta kai masu abubuwan da suka bukata na noma.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Gudun Hijira da Suka Koma Garuruwansu a Jihar Adamawa Na Shirin Yin Noma - 3' 41"