Majalisar Dinkin Duniya tace ‘yan gudun hijiran kasar Afghanistan su fiye da dubu 200 ne suka koma kasarsu daga Pakistan, fiye da rabinsu a cikin makkonin nan, duk da ganin yadda mayakan Taliban ke kara tsananta hare-haren da suke kaiwa a cikin Afghanistan din.
WASHINGTON, DC —
Wadanan alkalumman sun nuna cewa wannan itace jimillar yawan ‘yan gudun hijira mafi yawa da aka taba samu masu komawa Afghanistan tun shekarar 2007, lokacinda kamar ‘yan gudun hijira dubu 360 suka koma Afghanistan a karkashin wani shirin MDD.
Koda yake akwai dalilai da yawa da suke sa ana samun karin ‘yan gudun hijiran dake dawowa gida a Afghanistan, galibi duk komawar ta ganin-dama ce, a cewar Dunya Aslam Khan, wata wakiliyar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta MDD a Pakistan.
Sai dai har yanzu dai akwai ‘yan gudun hijiran Afghanistan kamar milyan daya da rabi dake zaman hallacci a kasar ta Pakistan, yayinda ake da wasu kamar milyan daya dake zaune ba bisa ka’ida ba.