Yan Gudun Hijira A Adamawa Na Kukan A Mayar Da Su Jiharsu

'Yan Gudun Hijira Sun Yi Zanga Zangar Nuna Rashin Wadataccen Abinci A Jihar Borno

Yayin da hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana wannan shekara ta 2016 da cewa itace mafi muni ga 'yan gudun hijira da 'yan cirani, yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu daga jihar Borno, da yanzu ke sansanin yan gudun hijira a jihar Adamawa, sun bukaci da a hanzarta a maida su jihar su ta Borno.

Yan gudun hijiran sun koka ne game da halin kuncin da suke zargi suna ciki, zargin da hukumar NEMA ke musantawa.

Kamar sauran kasashe Najeriya na da dubban yan gudun hijiran dake neman komawa garuruwansu sakamakon halin kunci da suke zargin cewa suna fama da shi a yanzu, kamar yadda wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz ya tarar a sansanin yan gudun hijira dake Fufore a jihar Adamawa dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Mallam Habu Abdullahi dake zama shugaban yan gudun hijiran dake wannan sansani. Cewa yayi “Mu Gaskiya abin da suke yi mana suna shiga hakkin mu. Abin da yasa na ce haka shine; na daya basa bamu isashen abinci, asibiti babu magani. Abincin da suke bamu ba yadda yake wani lokaci abincin da tsutsa sai kace fursuna.”

Ya ci gaba da cewa lafiyarsa kalau ya je sansanin amma yanzu kusan watanni Uku kenan yana fama da cutar gyambon ciki.

Shima wani yaro dake gudun hijira a wannan sansanin cewa yayi, basa samun abincin da yakamata duk da cewa abincin babu dandano, ga daukar lokaci.

Su kuwa wasu mata ciki har da masu shayarwa, cewa sukayi bukatar su itace a mayar da su jiharsu ta Borno.

To sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da majalisar dokokin jihar Adamawa ke haska fitillarta game da halin da yan gudun hijira da kuma wadanda suka koma yankunasu ke ciki. Hon. Hassan Barguma shine shugaban kwamitin kula da yan gudun hijira na majalisar.

Wanda yace zasu bi duk hanyar da ta dace don ganin cewa duk abin da aka tanadarwa yan gudun hijira ya kai garesu.

A bangaren hukumar kai dauki ta NEMA wadda itace ke kula da yan gudun jirar, tace tana nan tana kokari, a cewar Sa’ad Bello da ke zama jami’in hukumar mai kula da jihohin Adamawa da Taraba.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Yan Gudun Hijira Na Kukan A Mayar Da Su Jiharsu - 3'56"