'Yan Gudun Hijira 140 Daga Nijar Sun Isa Jihar Neja

Najeriya 'yan gudun hijira daga Nijar

'Yan gudun hijirar da jamhuriyar Nijar ta koro saboda rikicin 'yan kungiyar Boko Haram, dari da arbain ne suka isa jihar Neja dake tarayyar Najeriya mutanen dai wadanda masu sana'ar kamun kifi ne a yankin Diffa dake kasar jamhuriyar Nijar, 'yan asalin jihar Neja ne da suka je can domin gudanar da sana'ar su na kamun kifi.

Shugaban tawagar ;yan gudun hijirar Malam Abubakar Usman yace sun tabka hasara mai yawa tare da ganin wahala iri-iri kafin isowar sun gida jihar Neja.

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja ce tare da jami'an tsaro ke aikin tantance wadannan mutane, kuma tuni an gano cewa 'yan asalin kananan hukumomi bakwai ne dake cikin jihar Neja.

Daga cikin wadannan mutane dai an samu 'yan asalin jihar Kogi da kuma na babban birnin tarayya kuma tuni an tura su zuwa garuruwansu.