Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsarin Ilimin Bai-Daya na Shan Suka a Kasar Amurka


Yara 'yan makaranta
Yara 'yan makaranta
Tun a shekarar 2009 kimanin shekaru shida da suka gabata, an samar da wani tsari a nan kasar Amurika, don dai daito a bangaren ilimin Firamari a fadin kasar baki daya. Shi dai wannan tsarin da a kayima lakani da “Tsari na Kowa” wato mahinmancin wannan tsarin, shine a samar da hanya daya tilo wadda za’a dinga koyar da karatun Turanci, English da lissafi, Mathmatic. Wato abun nufi a nan shine, duk wani abu da bashi a cikin tsarin to babu damar a koyar da shi komi mahimancin shi. A hakane wasu masana ke gani cewar wannan tsarin bazai ciyar da ilimi gaba ba a matakin farko wato Firamari. A wata kasida da wata Farfesa. Me suna Sandra Stotsky, ta gabatar, tayi nuni da cewar lallai wannan tsarin na bukatar gyara, ganin yadda yanzu an watsar da wasu tsare-tsare na koyar da al’adu, wasan kwai-kwayo a cikin manhajar koyon turanci, don haka wannan da sake. A zahirin gaskia wannan tsarin ba zai ciyarda ilimin firamari gaba ba, a daukacin kasar Amrka, a cewar ta.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG