‘Yan Majalisar wakilai na bangaren Democrat, sun kaddamar da wani gagarumin bincike kan kwamitin yakin neman zaben shugaba Donald Trump a zaben 2016, da harkokin kasuwancinsa da lokacin da aka mika mai mulki, tare da yin dubi kan ko shugaban ya hana doka ta yi aiki kan bincikensa da ake yi.
Kwamitin shari’a na majalisar ta wakilai, ya aika wa da mutum 81 da wasu kungiyoyi wasiku, wadanda suke da alaka da Trump, inda suka nemi a ba su takardu cikin mako biyu, kan batutuwa da dama da suka shafi shugaban na Amurka.
Shugaban kwamitin Jerrold Nadler, ya ce:
“Ya zama dole mu bayyanawa Amurkawa (abin da ya faru), ba za mu dogara da binciken da kwamitin Mueller ke yi ba, saboda ba mu san lokacin da za a kammala shi ba.”
Shi dai shugaba Trump ya jima yana musanta zargin cewa akwai wata alaka tsakanin kwamitin yakin neman zabensa da Rasha, kuma da aka tambaye shi kan wannan sabon bincike na kwamitin Nadler, sai ya ce, “zan ba da hadin kai, dadin abin shi ne, babu wata alaka, duk abin kage ne.”