Yan Dimokarat Sun Zargi Trump Da Take-Taken Danne Wani Kudurin Doka

Shugaban Amurka Donald Trump

‘Yan jam’iyyar Dimokarat a Majalisar dokokin Amurka sun zargi shugaban kasar Amurka Donald Trump da shugaban masu rinjaye na Majalisar dattawa, wandan dan Republican ne, da take-taken danne wani kudurin doka da aka gabatar da zummar kare zaben Shugaban Amurka na gaba daga duk wani katsalandan daga Rasha da sauran kasashe.

Sun kuma yi gargadin cewa saboda take-taken Trump da Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa dan Republican Mitch McConnells, lokaci na kurewa na samar da ingantaccen tsari gabanin zaben 2020.

“Da alamar shugaban masu rinjaye, bisa bukatar fadar White House, ya mai da take-taken murkushe duk wani kudurin doka mai inganci a matsayin babban abin da ya sa gaba,” a cewar Mark Warner, mataimakin shugaban kwamitin leken asiri, yayin zantawa da manema labarai lokacin wani taron manema labarai a ginin Majalisa jiya Talata.