'Yan Democrat Sunyi Wa Bernie Sanders Cha A Wata Muhawara

Masu fafutukar neman shugabancin Amurka na jam’iyyar Democrat sun yi wa dan takara Bernie Sanders Cha a yayin wata muhawara da aka yi mai cike da rudani a daren ranar Talata.

Bernie Sanders

Yayin muhawarar, abokan karawar Sanders sun yi ikirarin cewa, mutumin da ya bayyana kansa a matsayin dan Democrat mai ra’ayin ‘yan gurguzu ba zai iya kayar da Shugaban Amurka Donald Trump na jam'iyyar Republican ba a zaben shugaban kasa da za’ayi a watan Nuwamba, idan ya zama dan takarar jam’iyyar.

Abokan adawar Sanders mai shekara 78 da haihuwa, sun yi ta caccakar shi daya-bayan-daya, suna tuhumarsa da nuna goyon baya ga shirin inshorar kiwon lafiya na gwamnati, wanda za a iya kashe dala tiriliyan 60 a cikin shekaru goma, da kawo karshen tsare-tsaren inshora masu zaman kan su da Amurkawa miliyan 160 ke amfani da su don biyan kudaden kula da lafiyar su.

Sun kuma yi ta hantarar Sanders saboda adawa da ya nuna kan wani kuduri da aka gabatar a Majalisa, wanda zai dora alhakin matsalar harbe-harben bindiga da ke yawan faruwa a Amurka akan kamfanonin da ke kera makamai.

Sanders ya kare matakin amincewa da ya yi da shirinsa na "Medicare for All", wato inshorar lafiya da kowa-da-kowa zai mora, yana mai cewa tsarin zai rage kudaden kiwon lafiya ga miliyoyin Amurkawa.

Sai dai ya amince cewa ya yi kuskure da ya kada kuri’ar kin amincewa da kudurin dokar tsaurara matakan mallakar bindiga.

Sanders, dadadden dan majalisar dattawa daga jihar Vermont da ke arewa maso gabashin Amurka, wanda shi ne dan takarar da ya fi samun kuri’u a zabukan sharar fage da aka yi na jam’iyyar Democrat, ya kasance dan takara na gaba-gaba a binciken jin ra’ayin jama’a da aka yi.

Amma abokan hamayyarsa sun ce manufofinsa sun yi hannun riga da muradan Amurkawa, inda suke ikirarin cewa, zai iya dishe damar da jam’iyyar Democrat ke da ita ta samun kujerun majalisar dokokin kasar.