Shugabar Majalisar Wakilan Amurka, Nancy Pelosi, ta ce matakin da Shugaba Donald Trump ke so ya dauka na tura karin dakaru da makaman dakile hare-haren sama zuwa Saudiyya da Hadaddiyar Dular Larabawa, shiri ne na baya-bayanan da shugaban ke so ya aiwatar ta hanyar tsallake majalisar dokokin Amurka domin yin gaban kansa.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Sakataren tsaron Amurka Mark Esper da babban hafsan hafsoshin dakarun kasar, Janar Joseph Dunford, suka bayyana cewa, Shugaba Trump ya aminta da wannan mataki.
A cewar Esper, aniyar tura dakarun da makaman, ta biyo bayan taimakon da kasashen biyu suka nema ne daga Amurka, domin inganta matakan tsaron sararin samaniyarsu, bayan harin da aka kai kan matutun man kasar ta Saudiyya.
Mayakan 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun dauki alhakin kai wannan hari, amma Amurka ta ce Iran ce da alhaki, zargin da hukumomin Tehran suka musanta.