Tun farko dai a wata wasika da ta aikewa manema labarai babbar jam’iyyar Adawa ta PDP, ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da shigar da ‘yan daba daga jihohin Zamfara da Katsina da Filato da kuma sauran makwabtan jihohi.
Haka kuma jam’iyyar PDP ta bayyana cewa a wasu mazabu an hana jami’anta damar yin aikinsu na saka ido a harkokin zaben. Wanda hakan ne ya sa ta yi kira ga hukumar zabe INEC ta soke zaben na Kano.
A ‘daya bangaren, jam’iyyar APC a ta bakin mataimakin shugabanta na jiha, Shehu Maigari, ya yabawa ‘yan jam’iyyar APC ga hadin kan da suke baiwa jami’an tsaro, wanda hakan yasa zaben ke gudanar lafiya. Ya kuma yi watsi da zarge-zargen da PDP take kan zaben.
Shaidun gani da ido sun bayyanawa Muryar Amurka yadda suke ganin ‘yan daba dauke da muggan makamai suna cin karensu babu babbaka, duk kuwa da jami’an tsaron da aka ajiye a mazabu daban-daban.
Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Kano bata fito ta ce komai ba kan abin da ke faruwa a jihar.