'Yan Boko Haram Sun Sauya Salon Hare-harensu a Jihar Adamawa

A cikin ‘yan kwanakin nan rahotanni na nuna cewa mayakan kungiyar Boko Haram suna sauya salon kai hare-harensu ciki har da kisan dauki daidai, da kuma na sari-ka-noke, da kona kauyuka ko kuma dasa bama bamai a gonaki.

Wannan sabon salon yanzu haka ya sake jefa jama’ar yankunan da aka kwato a garuruwan Madagali da Michika daga hannun ‘yan Boko Haram cikin wani yanayi na dar-dar, da har ya kai ga wasu sake yin gudun hijira.

Honarable Yusuf Muhammad, shugaban karamar hukumar Madagali mai barin gado ya bayyana halin da suke ciki a matsayin abin takaici. Ya kuma ce, akwai jami'an tsaro wurin don ko a cikin makon nan sai da suka kashe wasu manyan mayakan Boko Haram ko da yake dai ana cigaba da kai masu hari, kuma yawan jami’an tsaron bai isa ba.

Mr. Adamu Kamale, dan majalisar wakilai dake wakiltar Madagali da Michika a jihar Adamawa, yace suna iya kokarinsu wajen shawo kan wannan matsalar, to amma kawo yanzu ba su sami karin jami’an tsaron da suke bukata ba. Ya kara da cewa hatta abincin dake gonaki maharan basu bari ba, abin ya kai ga mutane na jin tsoron fita gona.

Su ma hukumomin tsaro a jihar Adamawa sun ce suna nasu kokarin don kare rayukan jama’a a cewar SP Othman Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar. Ya kuma kara da jan hankalin mutane akan su sa ido sosai idan zasu shiga gona, ko su sanar da jami’an tsaro idan suka ga wani abu da basu gane ba.

Ga karin bayani a cikin sauti daga Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Boko Haram Sun Sauya Salon Hare-harensu a Jihar Adamawa - 3'26"