Wakiliyar Muryar Amurka a zantawar da tayi da mutane daban daban daga jihar Borno ta gano cewa 'yan Boko Haram sun dade suna satar mutane musamman 'yan mata da kuma maza matasa ko wadanda suke da sauran kuzari.
Wani daga Gwoza 'yarsa na cikin wadanda 'yan Boko Haram suka sace yau fiye da shekara daya. Yace a garin Wala, banda tashi diyar 'yan Boko Haram sun kwashi 'yan mata goma sha takwas. Daga baya kuma sun sake dawowa sun kwashi guda takwas. A Gwoza an kwashi samari fiye da dubu daya. Wasu suna gida aka kai samame aka kamasu. Wasu kuma suna bakin rijiyar gidansu . Duk wadanda aka sace babu labarinsu.
Wani kuma da bai ambaci sunansa ba yace diyarsa na dawowa ne daga makaranta aka saceta kimamnin watanni tara yanzu. 'Yan Boko Haram din sun yi anfani da wayar hannunta sun kira mahaifinta. Sun fadawa uban sun aurar da ita wai domin mahaifinta bai aurar da ita ba ya sata makaranta. Sun ce yayi hakuri sun riga sun daura mata aure bisa ga nasu hukuncin. Ya gayawa jami'an tsaro amma babu abun da aka yi. Haka ma wasu 'yan mata biyu suna dawowa daga makaranta sai suka sacesu.
Akwai yara maza matasa wajen dubu uku da aka sace wadanda tamkar yanzu basu da 'yanci. Mutanen yankin sun ce suna tsoron abun da ka iya faruwa da 'yan yara kanana da suke dasu yanzu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5