Alhaji Umar Zanna Mustapha ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci 'yan gudun hijira dake garin Gombe inda ya mika godiyar gwamnatin jihar ga gwamnan Gombe Hassan Dankwambo da jama'ar Gombe domin karbar 'yan Damboa da kuma tanada masu.
Yace ba sonsu ba ne su zauna a garin wasu illa jarabar da ta addabesu. Yace ya kwashe kusan sa'o'i ashirin da shida yana kan hanya daga Maiduguri zuwa Gombe domin ya ziyarci wasu 'yan gudun hijiran dake wasu wurare a Borno da Adamawa. Yace gwamnan jihar ya aikoshi ya ga yadda suke rayuwa kana ya bayyana masu shirin gwamnati.
Ya shaida masu cewa sojoji sun sake kwato garin Damboa kuma kura ta lafa. Daga wannan lokacin maza su fara shiri su tafi Damboa domin su soma gyara muhallansu kafin su kwashi matansu da 'ya'ya. Daga yau gwamnatin ta Borno zata fara shirya motoci domin mutane su fara komawa gidajensu. Gwamnan Bornon yayi alkawarin ba iyalan duk mutumin da aka kashe taimakon nera dubu dari biyu da hamsin. Kudin ba na sayan rai ba ne, illa dai taimako ne. Wadanda suka rasa gidajensu za'a taimaka masu domin su sake ginasu.
Mataimakin gwamnan yayi addu'ar samun zaman lafiya a jihar Gombe da Borno da Najeriya gaba dayanta.
Su 'yan gudun hijiran sun yabawa gwamnatin jihar Gombe da al'ummarta sabili da irin karbar da aka yi masu. Sun ce zasu koma Damboa amma ba zasu iya kai iyalansu ba yanzu. Sun yadda gwamnati ta koma dasu amma ba tare da iyalansu ba tukunna. Zasu koma idan babu hare-hare tsakanin Damboa da Biu da Uba Askira domin an kai masu hare-hare sau hudu. Harin na karshen nan da aka kai masu an kashe mutane da dama da basu iya binnesu ba sun barsu har gawarwakinsu suka rube. Cewa su koma yanzu ba zai yiwu ba sai idan babu hare-hare a garuruwan dake makwaftaka da Damboa.
Ga rahoton Sa'adatu Mohammed Fawu.