Bayan harin hankulan mutane sun soma kwantawa domin ana cigaba da zirga zirga akan hanyar.
Harin kwantar baunan ya auku ne jiya, lamarin da ya sa mutane da dama suka dage tafiya jiya bayan jin labarin harin, wasu kuma suka dauki doguwar hanya.
Amma yau an cigaba da yin zirga zirga kan hanyar musamman kan hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Biu har ta hada da jihohin Gombe da Adamawa da Taraba.
Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Kanar Sani Kukasheka shi ya fitar da sanarwar da ta tabbatar da harin. Yace sun tura wasu jami'an sojoji domin gano inda mutanen suka shiga.
Wannan harin shi ne na baya bayan nan tun harin da aka kai kan tawagar Majalisar Dikin Duniya da ta tashi daga Bama zuwa Maiduguri a watan jiya.
Muryar Amurka ta zanta da Alhaji Inusa Bama shugaban kingiyar direbobi na tashar Kano dake cikin Maiduguri, tashar da nan ne motoci ke tashi zuwa su Bama, Damboa da wasu wuraren. Yace su har yanzu suna bin hanyar da 'yan Boko Haram suka kai hari. Yace sun dogara ga tabbacin da jami'an tsaro suka basu na karesu da dukiyoyinsu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5