'Yan Boko Haram Na Tserewa Zuwa Wasu Kasashen Afirka

Biyo bayan hare haren da dakarun Najeriya da kuma sojojin hadin gwiwa na kasashen yankin Chadi suka kai kan sansanonin mayakan boko haram, yanzu mayakan na guduwa zuwa kasashen Sudan da jamjuriyar Afirka ta tsakiya.

Hedkwatar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram da na IS na tserewa daga yankin tafkin Chadi zuwa kasashen tsakiya da arewacin nahiyar Afirka.

Kakakin hedkwatar sojin Najeriya Kanar Sagir Musa, ya ce wannan na faruwa ne bayan luguden wuta da sojin Najeriya da na kawancen yankin tafkin Chadin sukai yi a baya bayannan.

Farmakin na manyan bindigogin da kuma jiragen saman yaki, a sansanonin 'yan ta'addan, yayi tsananin da akan dole suka kara gaba zuwa kasashen Sudan da Afirka ta tsakiya.

Janar Sagir Musa, ya ce tuni kuma rundunar dakarun kasashen yankin tafkin Chadi ta Sanar da wadancan kasashen don daukar mataki yayin da su ma sojin kasashen tafkin Chadin ke zama cikin shirin ko ta kwana.

A cewar Tsohon babban kwamandan Runduna ta 7, Manjo Janar Junaid Bindawa da a baya ya jagoranci yaki da 'yan Boko Haram, ya ce wannan ci gaba ne da ka iya kawo karshen yan ta'addan.

Shi ma wani jami'in tsaro Janar Sale Bala, ya ce ko da yake luguden wuta abu ne mai kyau, amma akwai bukatar a hada da yakar akidar 'yan ta'addan.

Ga karin bayani cikin sauti.