Wasu mayakan Boko haram ‘yan asalin kasar Chadi sun yi saranda tare da mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.
Abu Abor dan shekaru 61 da Abubakar Hassan dan shekaru 51, sun yi saranda ga dakarun sojin Najeriya na babban sansanin sojojin na goma sha daya dake Gamborun Ngala a jihar Borno.
Kanar Aminu Iliyasu, Mai Magana da yawun sashin aikace – aikace na hedikwatar sojin Najeriya, ya ce, binciken farko da suka gudanar ya tabbatar da cewa mayakan na bangaren shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, sannan suna zaune a wani matsuguni da suke kira Bagadaza, a zirin tafkin Chadi.
A 'yan watannin da suka gabata sojojin Artillery na Najeriya suka ta kai munanan hare hare ga sansanonin 'yan ta'addan, al'amarin da ya daidaita su tare da kassara su.
Abdullahi Aliyu Katsina, shugaban kungiyar samar da kyakkyawan shugabanci da tsaro a Nijeriya, ya yabawa sojojin Najeriya, sannan ya yi kira da cewa, ya kamata su dauki sabbin matakan yaki da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5