‘Yan bindigar da suka sace dalibai sama da 100 a makarantar sakandare ta Bethel Baptist a jihar Kaduna, sun tuntubi hukumomin makarantar.
A ranar Litinin ‘yan bindigar suka far wa makarantar ta Bethel suka kwashe dalibai da dama bayan wani artabu da suka yi da jami’an tsaron da ke gadin makarantar ta kwana, wacce ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia.
Rahotannin farko sun nuna cewa dalibai 165 aka yi garkuwa da su, amma mai makarantar Rev. Yahaya Adamu Jangado ya fadawa manema labarai a ranar Talata cewa, ‘yan bindigar sun tuntube su, kuma sun tabbatar masu cewa daliban da ke hannunsu su 121 kuma suna nan lafiya kalau.
“Mun samu kira daga ‘yan bindigar, kuma sun tabbatar mana cewa daliban suna cikin koshin lafiya.” Rev. Jangado ya ce kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewar Rev. Jangado, har sun samu damar tattaunawa da wasu daga cikin daliban.
“Sun kirga kansu, su 121 ne, da muka hada da adadin wadanda aka kubutar, sai muka ga adadin ya yi daidai.”
Sai dai babu wani karin hasken kan ko 'yan bindigar sun nemi a baya su kudin fansar daliban.
A ranar Talata iyayen daliban suka dunguma zuwa makarantar don neman karin haske kan halin da ‘ya’yansu ke ciki.
Sun kuma gudanar da taron addu’o’i don neman Allah ya kubutar masu da ‘ya’yansu lafiya.
An ga wasu daga cikin iyayen sun ajiye takalman ‘ya’yan nasu a farfajiyar makarantar yayin da wani Fasto ya jagoranci addu’o’in.
“Rufai (gwamnan Kaduna) ka dauki mataki, mun gaji,” wata mahaifiya ta ce tana kuka.
Gwamnatin jihar ta Kaduna wacce a ‘yan watannin ta fada kangin masu garkuwa da mutane, ta yi Allah wadai da wannan satar dalibai na baya-bayan nan, tana mai cewa tana iya bakin kokarin wajen ganin ta shawo kan lamarin.
Iyayen Daliban Da Aka Sace A Najeriya, Aun Gudanar Da Addu’o’i
Your browser doesn’t support HTML5