Ana ci gaba da zaman dar-dar a garin Ughelli dake jihar Delta bayan da wasu da ba a san ko su waye ba kawo yanzu suka kai wani mummunan hari akan wasu masallata a wani masallaci a garin na Ughelli, a baya bayan inda bayanai suka nuna cewa an jikkata mutane da dama, tare kuma da yin awon gaba da na’ibin limamin masallacin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta ce akalla mutane bakwai ne suka jikkata kuma tuni aka garzaya da su asibitoci daban-daban domin kula da lafiyar su. Haka kuma rudunar ta ‘yan sanda a jihar Delta ta ce ta tura jami’anta daban-daban inda lamarin ya faru domin ganin an kamo wadanda suka aikata wannan ta’asar.
“To lallai mun tura ‘yan sanda da wanda suke saka kaya da wanda basa saka kaya an shiga bincike,sannan na biyu kuma mun zuba ‘yan sanda a kasa a massalacin don muga hakan bai sake faruwa ba.. in ji Alhaji Badamasi Saleh shugaban ‘yan Arewa” in ji Muhammad Ali Kwamishnan rundunar ‘yan sanda jihar Delta.
Kawo yanzu dai ‘yan asalin arewacin Najeriya dake gudanar da harkokinsu na yau da kullum a garin da Ughelli na ci gaba da zaman zullumi da suke ciki.
“Mutanenmu mazauna jihar Delta a wata karamar hukuma da ake ce mata Ughelli suna nan sun gama sallar asuba ana musu nasiha sai wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka shigo sai suka je suka kama wuyar taguwar liman suka ce da shi ya zo a tafi, sai kuma suka bude musu wuta anan take suka harbi mutanen mu..” In ji Alhaji Badamasi shugaban ‘yan arewa mazauna jihar Delta.
Masu sharhi akan harkokin yau da kullum sun fara tsokaci dangane da tabarbarewar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.
“ Yan sanda da jami’an tsaro, Jami’an soja da jami’an 'yan sandan ciki wato SS da kansu ya rataya, su yi bincike su fitar da rahoto da sakamakon binciken da su ka yi kan tabarbarewar tsaro da hare haren da ake kai wa a wurare daban na kasar nan, abubuwan dake gabansu sun fi karfin su," In ji Farfesa Yahya Tanko Baba amai sharhi kan al’amuran yau da kullum.
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar Sokoto
Your browser doesn’t support HTML5