‘Yan fashin dajin da suka sace dalibai da dama a ranar Laraba a makarantar sakarandare ta Kaya da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara a arewacin Najeriya, sun sako biyar daga cikin daliban.
Akalla dalibai maza da mata 73 ‘yan bindigar suka sace a makarantar ta je-ka-ka-dawo.
Tsohon kansila a mazabar Kaya Yahaya Kaya, ya fadawa gidan talabijin na Channels cewa, diyar kaninsa na daga cikin dalibai biyar da aka sako.
A cewarsa, an kai yaran duka su biyar garin Kaya da misalin karfe daya na safiyar ranar Alhamis.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara ya kuma tabbatarwa da Channels cewa, lallai an sako dalibai biyar, inda ya kara ba da tabbacin cewa za a sako sauran ma.
Jaridar Premium Times ta yanar gizo ta ruwaito wani babban jami'in makarantar yana cewa daliban tserewa suka yi.
Satar daliban makarantar ta Kaya, ita ce ta baya-bayan nan da ‘yan bindigar suka yi a jihar ta Zamfara.
A watan Fabrairun bana, sun sace dalibai mata 279 a makarantar sakandare ta Jangebe da ke jihar ta Zamfara. Ba a sako su ba sai a watan Maris.
Satar daliban makarantar na Kaya na zuwa ne kwanaki bayan da aka sako daliban Islamiyya na makarantar Salihu Tanko da ke Tegina a jihar Neja, wacce ita ma ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane.
Yankin arewa maso yammacin Najeriya ya jima yana fama da matsalar ‘yan fashin daji wadanda suka addabi mutane da satar jama’a don neman kudin fansa.
Hukumomin yankin sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen shawo kan matsalar, amma duk da haka al’amura sai kara dagulewa suke yi kamar yadda masu lura da al’amura ke cewa.
Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
Your browser doesn’t support HTML5