A Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya, bayan harin da mahara suka kai Gwadabawa inda suka sace basaraken Mammande da mutane 6, a farkon wannan mako, sai gashi sun sake afkawa garin na Gwadabawa inda suka sace mutane goma sha daya.
Shugaban karamar hukumar Aminu Aya ya maganta akan sabon harin.
Bayan daukar mutanen daga Gwadabawa, maharan sun tafi da su ta hanyar Dambar dikko dake cikin yankin Illela wadda ke makwabtaka da Gwadabawar inda jama'ar garin suka tarbe su.
Shugaban karamar hukumar ta Illela Injiniya Aliyu Salihu yace lokacin ne aka yi bata-kashi tsakanin maharan da mutanen garin na Damba.
Rundunar 'yan sandan Najeriya dai ta kasa yiwa jama'a bayani akan dukkan hàre-hare da ake kaiwa jama'a kwananan yankuna daban daban,duk lokacin da manema labarai suka tuntubi kakakin rundunar DSP Sanusi Abubakar baya daukar kiransu, duk da yake jama'ar da hare-haren ke faruwa wurin su suna tabbatar da cewa ‘yan sanda na da masaniyar hare-haren.
Jama'ar yankunan da ke fama da matsalolin dai na ci gaba da kokawa musamman ganin yadda matsalolin suka hana yin noma a wasu wurare, kamar yadda tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni Abdullahi Muhammad Tsamaye ke kokawa.
Masana lamurran tsaro dai sun jima suna bayar da shawarwari ga mahukunta akan yadda za'a shawo kan lamarin, yayinda matsalolin ke ci gaba da wanzuwa.
Sauri cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5