Wasu rahotanni na cewa an kashe mutanen da suka zarce 50 a kauyen Izghe dake yankin karamar hukumar Madagali, mai iyaka da dajin da ake kyautata zaton nan 'yan Boko Haram suke
WASHINGTON, DC —
Kasa da kwanaki 4 a bayan da 'yan bindiga suka yi kwanton-bauna suka kashe sojoji kimanin 9 a kauyen Izghe dake yankin karamar hukumar Madagali a Jihar Adamawa, an sake kai wani sabon farmaki cikin daren nan a kauyen dake bakin iyakar Adamawa da Borno.
Wasu majiyoyi da mutanen garin sun ce an kashe mutanen da suka zarce hamsin a wannan farmakin, amma kuma ba a ji ta bakin sojoji ko gwamnatin jihar Adamawa kan wannan adadin ba.
Mazauna kauyen suka ce a cikin dare wadannan 'yan bindiga, wadanda ake kyautata zaton 'yan kungiyar na ta Boko Haram ce, suka far ma kauyen inda suka yi ta yanka mutane tare da harbi.
An ce mutane da dama sun tsere suka bar kauyen cikin dare.
Kauiyen na Izghe da kuma yankin karamar hukumar Madagali a jihar ta Adamawa, suna iyaka da wani makeken dajin dake cikin jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda a nan ne ake kyautata zaton 'yan Boko Haram suke da sansanoni.
Dukkan garuruwan da ake kai ma hari, kamar Benisheikh, Maiduguri, Konduga, Bama, Gwoza, Damboa, Madagali, su na kewaye da wannan dajin ne.

Your browser doesn’t support HTML5