Rahotanni daga jihar Zamfara da ke Arewa maso yammcin Najeriya na bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a wata makarantar sakandaren jeka-ka-dawo, inda suka yi awon gaba da dalibai kusan 100 na makarantar.
Wasu majiyoyi sun shaidawa Muryar Amurka cewa maharan sun kai farmaki a karamar sakandaren ta jeka-ka-dawo da ke garin Kaya a cikin karamar hukumar mulkin Maradun da safiyar Laraba, bayan dalibai sun kammala hallara domin darussa na yau da kullum.
Duk da yake ba'a kai ga tantance adadin daliban da 'yan bindigar suka sace ba, amma majiyoyin sun ce ana sa ran akalla sun kai 100.
Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
Your browser doesn’t support HTML5
Wannan na zuwa ne 'yan kwananki bayan sako wasu daliban jihar da aka sace a Bakura, duk da yake wasu rahotanni na bayyana cewa har kawo yanzu akwai wasu daliban jihar da ke hannun 'yan bindiga.
Hakanlamari kuma ya auku ne kwana 3 bayan da gwamnatin jihar ta ba da sanarwar kafa wasu dokoki, da suka hada da rurrufe kasuwanni da takaita zirga-zirga a duk fadin jihar da ake hasashen ta fi ko wacce fama da kalubalen tsaro.
A can baya dai gwamnatin jihar ta rungumi shirin sulhu da 'yan bindigar da ke kai hare-hare, kisan jama'a da satar mutane domin karbar kudin fansa, duk kuwa da kakkausan suka da shirin ya fuskanta daga bangarori daban-daban, ciki har da gwamnatin tarayya.
To sai dai daga baya gwamnatin ta dawo daga rakiyar shirin na sulhu, kana ta ci gaba da daukar wasu matakai na dakile ayukan 'yan bindiga a jihar.
Za mu kawo muku cikakken bayani kan lamarin nan gaba kadan.