Maharan sun kutsa jami'ar ne da misalin karfe goma na dare inda suka shiga kasuwar da ke cikin jami'ar suna harbi a iska, abin da ya tayar da hankalin masu shaguna da sauran jama'ar da ke cikin kasuwar kuma kowa ya yi ta kansa.
Shugaban jami'ar Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis ya ziyarci jami'ar a cikin daren Litinin domin kwantar da hankalin dalibai, ko da yake a cewar jami'ar ba 'yan bindiga masu satar mutane ba ne, barayi ne kawai suka zo satar abinci a kasuwar dake cikin jami'ar. Tuni dai jami'ar ta dauki matakan kara karfafa tsaro a cikin wurin.
Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Sokoto a fannin tsaro Kanal Ahmad A. Usman mai ritaya ya tabbatar da wannan harin, sai dai ya ce dabarun 'yan bindiga na saka shakku da firgita a zukatan jama'a ne, saboda sun ga an tasar musu ta ko'ina.
A cewarsa matakan tsaron da ake daukao ba abu ne da ake bayyana wa a bainar jama'a ba, amma dai gwamnati tana kan daukar matakai don kawar da kalubalen.
Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da addabar jama'a a sassan Najeriya, don ko a makon nan rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kisan mutum uku da kuma raunata wasu mutane a wani hari da ya haddasa tashin hankali tsakanin al'ummomi biyu a yankin karamar hukumar Binji, kamar yadda kakakin rundunar a Sokoto ASP Ahmad Rufa'i ya tabbatar.
Mahukunta dai na cewa suna daukar matakai kuma ana ganin nasara ga wasu matakan da ake dauka na dakushe ayyukan 'yan bindiga.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5