'Yan Bindiga Sun Kuma Sace Dalibai A Kaduna

  • Murtala Sanyinna

Gunmen

Makarantar sakandaren ta Bethel dai makarantar kwana ce da ke wajen birnin Kaduna, kuma har kawo yanzu ba’a tantance adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ba.

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki a makarantar sakandaren Bethel da ke Marmara cikin yankin karamar hukumar mulkin Chikun a jihar Kaduna, inda kuma suka yi awon gaba da wasu dalibai da dama.

A cewar wani mai gadi a makarantar sakandaren ta Bethel, Daniel Muhuta, ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalign karfe 2 na safiyar Litinin, suka kuma soma harbi ba kakkautawa.

“Ina kwance a bayan dakunan kwanan dalibai na soma jin harbi, sai kuwa na kara labewa, kuma na sami tsira” in ji Muhuta.

Makarantar sakandaren ta Bethel dai makarantar kwana ce da ke wajen birnin Kaduna, kuma har kawo yanzu ba’a tantance adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ba.

To sai dai jami’an tsaro sun zagaye yankin da makarantar take, a yayin da kuma iyaye da ‘yan uwan daliban da aka sace suka soma tattaruwa a bakin kofar makarantar suna alhinin abin da ya faru.

Kawo lokacin wallafa wannan labarin kuma ba wani bayani daga gwamnati ko hukumomin tsaro dangane da wannan al'amari.

Lamarin ya faru ne kwana daya bayan sace wasu mutane akalla 8, a wani farmakin da 'yan bindiga suka kai a asibitin kutare ta gwamnatin tarayya a jihar ta kaduna.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake kai farmaki tare da yin awon gaba da dalibai ba a jihar Kaduna.

Haka kuma wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da har yanzu daliba makarantar Islamiyyar Tegina a jihar Naija, da na kwalejin gwamnatin tarayya ta Yawuri a jihar Kebbi, suke ci gaba da kasancewa a hannun 'yan bindigar, bayan makwanni da sace su.