Wasu 'yan bindiga sun sace matan wani basarake biyu da 'ya'yansa shida, inda suka kashe matan da 'ya'ya biyar bayan da suka nemi kudin fansa ba a basu ba. Daya daga cikin 'ya'yan ya tsira bayan da aka harbe shi amma ya samu ya tsere.
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da aukuwar lamarin a ta a bakin kakakinta SP Usman Abdullah. Ya kuma ce rundunar ta na iya kokarinta don ganin an kamo masu hannu a mummunan lamarin.
Wani dan garin Mutun Biyu wanda aka yi jana'izar gawarwakin a idonsa mai suna Aliyu Mutum Biyu, ya ce sun binne mutane bakwai a wuri guda saboda gawarwakin sun fara rubewa kafin a gano su.
Kwamanda Ahmad Muhammad, wanda ya jagoranci tawagar 'yan bangar da ta je dajin da aka dauko mutanen, ya shaida wa Muryar Amurka cewa sun ga harbin bindiga a jikin gawarwakin mutanen.
Ishiyaku Umaru Tammai, na daya daga cikin 'yan bangan da suka gano daya daga cikin 'ya'yan basaraken da ya tsira da ransa, ya ce a lokacin da suka ga yaron ba ya iya tafiya sai dai rarrafe kuma ya bayyana musu cewa masu garkuwan sun kashe sauran 'yan uwansa.
Saurari rahoton Salisu Lado:
Your browser doesn’t support HTML5