NIAMEY, NIGER - Lamarin ya faru ne da rana tsaka a jiya Laraba lokacin da ‘yan bindiga suka tare wata motar jigilar kamfanin STM a wani wurin dake a tazarar km 5 da tashar binciken kan iyakar Nijar da Burkina FASO wato a tsakanin kauyen Fono da kauyen Zelangue na biyu a gundumar Tera . Rahotanni na nuni da cewa, maharan sun hallaka akasarin wadanan fasinja.
Motar kirar bas mai dauke da fasinja 43 ta fito ne daga birnin Ougadougou cikinsu har da ‘yan sanda uku da ke shirin komawa gida bayan kammala aikin mako-mako a tashar binciken iyaka.
Ku Duba Wannan Ma Mutuwar Wani Soja Ta Haifar Da Cece Kuce Yayinda Rahotanni Ke Cewa Hukumomin Nijer Sun Kama Wasu SojojiRahotanni sun yi nuni da cewa, ‘yan bindigar sun kona motar sannan su ka karkashe mutanen dake cikinta in ban da wasu mata uku da suka tsira da ransu yayinda daya daga cikin ‘yan sandan uku ya ji mummunan rauni.
Magajin garin Tera, Hama Mamoudou ya tabbatar da faruwar wannan al’amari. Koda yake ya ce ba shi da masaniya game da zahirin adadin mutanen da suka rasu sanadiyar wannan hari.
Haka kuma maharan sun kona wata mota kirar telem wato Trela Tuni aka kwashe gawarwakin wadanan mutane aka ajiye su a dakin ajiyar gawa na asibitin Tera domin aikin tantancewa kafin a nan gaba a yi jana’izarsu ko kuma a damka su ga danginsu.
Your browser doesn’t support HTML5
Kamfanin jigila na STM ya tabbatar da faruwar wannan al’amari haka kuma Muryar Amurka ta yi katari ganin wata kanwar dreban da abin ya rutsa da shi ta isa a cibiyar kamfanin na STM cikin sheshekar kukan wannan rashi.
Wannan shine karon farko da ‘yan bidigar yankin Tilabery ke tare motar fasinjoji, abinda ke nunin yadda masu tada kayar baya ke kokarin karkatar da ayyukansu wajen huce takaici akan fararen hula wanda masana sha’anin tsaro ke kallonsa a matsayin wata alamar dake nunin jami’an tsaro sun ci karfin kungiyoyin ta’addancin iyakokin Mali, Nijar da Burkina Faso misalin yadda a bayan nan suka karkatar da ayyukansu wajen dasa nakiya akan hanyoyi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5