Wani jami’in gwamnatin Kwango ta Kinshasa yace ‘yan bindiga sun kai farmaki jiya lahadi a kan gidan shugaba Joseph Kabila, abinda ya haddasa fadan da ya kashe mutane akalla 7.
An ce shugaba Kabila bai samu ko da kwarzane ba a bayan wannan harin da aka kai kan gidansa dake wata unguwa mai suna Gombe a Kinshasa babban birnin kasar.
A wata hirar da yayi da Muriyar Amurka, kakakin gwamnati Lambert Mende, yace mayaka kimanin 50 ne suka kai farmaki a kan gidan shugaban. Yace su na dauke da manya da kananan bindigogi da kuma adduna.
Mende yace sojoji masu gadin shugaban sun tare wadannan mahara a wani wurin binciken ababen hawa suka kashe 7 daga cikinsu, suka kama wasu. Yace daya daga cikin masu gadin shugaban ya ji mummunan rauni a wannan fadan da aka yi kimanin mintoci 20 ana fafatawa.
Kakakin yace ba a san ko wannan harin na kokarin juyin mulki ne ko na ta’addanci ne ko kuma dai wani abin ne ba. Yace har yanzu ba a tabbatar da wadanda suka kai harin ba, amma jami’ai su na gudanar da bincike.
Shaidu sun ce sojojin dake gadin shugaban kasar, da wani tankin yaki akalla guda daya su na sintiri a unguwar a bayan wannan harin.