An hallaka Dr. Tiri Gyan ne a sabon harin da ‘yan bindigar suka kai da sanyin safiyar yau Talata.
Wani shaidan gani da ido ya shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho cewa, al’amarin ya faru ne da misalin karfe 1 da rabi na dare a gidansa dake karamar hukumar Dutsin-Ma ta jihar Katsina.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun mamaye unguwar da muggan makamai, suna harbin kan mai uwa da wabi, kana daga bisani suka yi awon gaba da 2 daga cikin ‘ya’yan malamin jami’ar.
Ku Duba Wannan Ma 'Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Shugaban Jami'ar Usman Danfodio Farfesa Saidu
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai yace nan bada jimawa ba rundunar zata fitar da cikakkun bayanai akan sa.
Dutsin-Ma na cikin kananan hukumomi 10 dake fama da hare-haren ‘yan bindiga kusan a kowace rana duk kuwa da kokarin gwamnatin Katsina da hukumomin tsaro ke yi na dawo da zaman lafiya a jihar.