Wasu ‘yan bindiga guda biyu sun harbe wasu jami’an ‘yan sanda guda 2 a lokacin da suke tuki zuwa wajen aiki a yammacin birnin Alkahira ta kasar Masar.
WASHINGTON DC —
Ministan harkokin cikin gidan kasar yace, an kawo ‘yan sandan zuwa birnin ne don gudanar da binciken harbin da aka yi ranar asabar a lardin Giza.
Rahotannin sun ce yan bindigara sun tsere sannan ba wanda ya dauki alhakin kai wannan harin akan ‘yan sandan. Harin ya biyo bayan harin da aka kai a wani Otal din kasar da ke mashakatar Hurghada a jiya juma’a.
Inda wasu mahara da wuka suka raunata wasu matane biyu ‘yan kasashen Austria da Sweden. Jami’an tsaro suka kashe mahari daya tare da raunata ragowar dayan.
Sun kuma bayyana wadanda aka kaiwa harin suna nan suna murmurewa. Masar dai na fama da yakar ta’addanci tun bayan hambarar da Shugaba Mohammed Morsi a 2013.