'Yan bindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da auka wa mazauna yankunan karkara, lamarin da ke sa jama’a barin kauyukansu zuwa manyan garuruwa dake kusa domin neman tsira da rayukansu.
A wata hira da Muryar Amurka, wata mata ta fadi cewa da maharan sun hallaka mijinta a kauyen Farin Shinge dake karamar hukumar Kontagora bayan haka suka yi awon gaba da wasu mutane, ciki har da abokiyar zamanta.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Kontagora Aliyu Ibrahim Makiga, wanda kuma yana daya daga cikin jami’an tsaron 'yan banga dake aikin sintiri a karamar hukumar, yace lamarin na bukatar a kai agajin gaggawa a wannan yanki.
Tun bayan hallaka sojojin Najeriya kimanin 30 a jihar ake ta ganin shawagin sojojin Najeriya a sassa dabam daban na jihar Neja, sai dai hakan bai hana wadannan 'yan fashin dajin ci gaba da auka wa mazauna yankunan karkara ba.
To amma gwamnatin jihar Neja tace tana kokarin shawo kan lamarin. Kwamishiniyar yada labaran jihar Hajiya Binta Mamman, tace sun dukufa domin kawar da wadannan mahara.
A yanzu fatan al’umma shi ne samun nasarar shawo kan wannan matsala a daidai wannan lokaci da kakar girbin amfanin gona ke kawo jiki.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5