'Yan Asalin Arewa Mazauna Legas Dole Su Yi Ragista

Wata mata akan kwale-kwale a Legas

Kwana kwanan nan gwamnatin jihar Imo ta fito da shirin yiwa duk 'yan asalin arewa ajihar ragista sai gashi gwamnatin Legas ma ta bi sawun jihar Imo.

Yayin da majalisar dattawa ke kokarin takawa gwamnatin jihar Imo birki bisa ga shirin yiwa 'yan asalin arewa dake jihar ragista sai gashi gwamnatin Legas ta bi misalin jiahr ta Imo.

Yanzu haka sarakunan 'yan arewa dake jihar ta Legas sun ce an umurcesu da su sanarda mutanensu duk inda suke cikin jihar da su samu katin dake dauke da bayani game da su.

A taron da 'yan arewan suka yi a gidan da ake kira gidan arewa dake unguwar Ebutte Meta sun ce wajibi ne duk wani dan arewa dake zaune a Legas ya samu katin shaida. Wadanda kuma suka ki yin ragistan idan jamai'an tsaro suka kamasu, su kuka da kansu. Shugabannin sun ce ba zasu sa baki wajem karbo su ba.

Alhaji Garba Cedi daya daga cikin shugabannin 'yan arewan mazauna Legas yace ba laifinsu ba ne. Kuma sun leka sun hango ita ce hanya kadai da ka iya fidda su daga musgunawar jami'an tsaro a cikin jihar. Yace gwamnati tace a yi ragistan. Kafin su yi dokar sun tara sarakunan Legas suka nuna masu abun da suke son su yi. Gwamnatin tace tana son tayi hakan ne domin ta san iayakacin mazauna jihar domin a san yawan ruwan da gwamnati zata bayar tare da hanyoyi.

Da aka shaida masa cewa ragistan nada nasaba da batun tsaro sai yace su dama suna son a san mutanen dake zaune a unguwarsu. Yace nema suka zo yi a jihar Legas ba domin zama 'yan tawaye ba ko 'masu tada hankali.

'Yan asalin arewa sun yi taro da kwamishanan 'yan sandan jihar Legas akan lamarin. Sarki Sani Kabiru shi ma mazaunin Legas an tambayeshi ko an gayyato wasu kabilun sai yace a gaskiya 'yan arewa su ne kusan kashi casa'in na duk wadanda suke Legas. Su ne aka kira. Yace bayan sun yi mitin da kwamishanan sun koma sun baiwa 'yan sandan shawara..

Daga bisani an kira kungiyar Boko Haram da ta yiwa Allah Ta daina aikin tadancin da ta keyi domin kasar take batawa.

Ga rahoton Ladan Ibrahin Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Asalin Arewa Mazauna Legas Dole Su Yi Ragista - 3' 21"