Yadda ake gudanar da dimokradiya a Najeriya tamkar kamar ba daga Amurka aka aro tsarin ba domin a Amurka ana bin dokokin kasa da aka shimfida. Amma a Najeriya abin ya sha ban-ban.
A Najeriya wanda yake ya zama mai bincike sai ya koma ya zama dan amshin shata ko kuma ya zama yaron wanda ya kamata yana tsawatawa a bisa tsarin doka.
A wasu jihohin ma gwamnatin ta iyalan gwamnan ne da ya hada da uwargidansa ko 'ya'yansa ko kannensa ko kuma iyayen gidansa. Idan wani abu ake so tilas ne sai an bi ta hannun daya daga cikin mutanen. Idan ba haka ba sunan wannnan abun rasasshe.
Wasu jami'an gwamnatin jihohi kafin ma su isa ofisoshinsu sai sun bi ta gidan gwamna, ko gidan shugaban karamar hukuma ko shugaban kasa domin gaida uwargidan mai girma. A wasu jihohin ma ko kanin gwamna ko dan gwamna yafi mataimakin gwamna iko.
Wannan lamarin bai takaita a jihohi ba domin uwargidan shugaban kasa an ga yadda ta tattaro jami'an gwamnatin jihar Borno ta sasu gaba tana fada masu abun da ya yi mata dadi kuma aka nunata ga duniya.
Wai shin uwargidan mai mulki kama daga kansila har zuwa shugaban kasa tana da wani kebeben iko ne a cikin dokar Najeriya. Farfasa Shehu Abdullahi Zuru malamin koyas da dokokin kasa a jami'ar Abujan Najeriya yace babu wata doka da ta baiwa matan masu rike da mulki cewa akwai wata rawa da zasu iya taka akan kujerun mazajensu.
Dr. Abubakar Sadiq mai sharhi akan harkokin yau da kullum yace abun dake faruwa rashin gaskiya ne da kuma zalunci. Wani lokacin mutane ne suke jawo irin hakan ya faru. Idan an zabi shugaban karamar hukuma ko gwamna ko an ba wani mukamin minista sai mutane su jawo matar suna nuna mata irin abubuwan da zata iya yi domin ta taimaki mijinta da kuma kanta.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.