Etienne Tshisekedi, ya fada wa taron magoya bayan sa cewa wajibi ne Kabila ya tattara yanasa -yanasa daga yanzu zuwa 19 ga watan Disamba domin barin Ofis.
Wa'adin mulkin dai na shugaba Kabila ya kare amma wata kotu a kasar tace yana iya ci gaba da zama har sai an gudanar da zabe.
Shugaban ‘yan adawan yace Kabila na jan kafa ne kawai domin ya tsawaita tsawon mulkin sa.
Shidai Kabila tun a cikin shekarar 2001 yake kan karagar mulkin, kuma a bisa tsarin dokar kasar zango biyu ne kawai yake da damar yi wanda kuma ya kawo karshe a cikin wannan shekarar.
Sai dai suma magoya bayan Kabila sun gudanar da nasu taron a wani wuri a ranar Juma'a cikin Kinshasa, inda suka yi kira da abar Kabilar yaci gaba da kasancewa kan karagar mulkin har na wani lokaci